1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan-wasa mafi tsufa a gasar kofin Duniya

Abba BashirMay 15, 2006

Bayani akan Dan-wasa mafi tsufa a gasar kofin Duniya.

https://p.dw.com/p/BvVS
Roger Milla
Roger MillaHoto: dpa

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Abdurrasheed Ibrahim Adamu, Jihar Gomben tarayyar Najeriya.Malamin ya ce , shin daga cikin “Yan wasan kwallon kafa na Duniya, wane dan wasa ne ya bayyana a gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da shekarun da suka fi na kowanne dan wasa yawa ?

Amsa: Tsohon dan wasannan na kasar Kamaru wanda ake kira da suna Albert Roger Milla, wanda aka haifa a ranar 20 ga watan Mayun 1952, shine dan wasan da ya bayyana a gasar cin kofin kwallon kafa da shekarun da suka fi na kowanne dan wasan kwallo yawa a Duniya.

A gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya da aka buga a kasar Amurka a shekarar 1994, Roger Milla shine dan-wasan da ya fi kowa tsufa a wadanda suka buga wannan kwallo, a kwallon da suka buga ranar 28 ga watan Yunin 1994, tsakanin kasar Kamaru da Kasar Rasha, a lokacin yana dan-shekara 42 da haihuwa. Kuma a yayin wannan wasa sai da ya zura kwallo a ragar kasar rasha wanda hakan ya sa ya zama dan-wasa mafi tsufa da ya ci kwallo a gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya.