1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Martani kan hari a Gaza

Mahmud Yaya Azare LMJ
May 12, 2021

Ana ci gaba da dauki ba dadi tsakanin Falasdinawa da Dakarun sojin Isra'ila, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke yin kira ga bangarori biyu da su mayar da wuka.

https://p.dw.com/p/3tJWd
Israel | Unruhen in Jerusalem
Dakarun Isra'ila sun mamayi Falasdinawa a Masallacin Al-aqsa da ke birnin KudusHoto: Ammar Awad/REUTERS

Jiragen yakin Isra'ila na ta ragargazar yankuna mabambanta a yankin Zirin Gaza, a wani mataki da kakakin sojan Isra'ila Jonathan Conricus ya ce na ramuwa ne ga rokokin da masu jihadi ke harba musu: "Mun mayar da martani da harba rokoki kan yankunan 130 na sojojin jihadi da ke Gaza. Akalla mun halaka mayakan Hamas da na Islamic Jihad 15. Za mu ci gaba da kai wannan farmakin har sai an daina harba mana rokoki. Domin kungiyoyin jihadi na Falasdinawa na ci gaba da harbao rokoki."

Karin Bayani:Masar ta bukaci a tsagaita wuta a Zirin Gaza

Rikici ya tsananta tsakanin Isra'ilan da masu fafutukar na Falasdinu, tun bayan arangamar Falasdinawan da 'yan sandan Isra'ila a Masallacin Al-Aqsa da ta faro tun daga muzaharar Juma'ar da ta gabata da bisa al'ada ke gudana a duk Jumma'ar karshen Ramadana, domin nuna bacin rai kan mamaya da kuma kafa Isra'ilan da Falasdinawan ke kallo a matsayin haramtacciya.

Bildergalerie Nahost Konflikt
Martani da rokoki kan Isra'ila daga Zirin GazaHoto: Jack Guez/AFP/Getty Images

Dakarun na Isra'ila sun mamaye Masallacin na Al-Asa tare da yin kan mai uwa da wabi ga Falasinawan da ke tsaka da sallah tun a ranakun karshen mako, lamarin da ya fusata kungiyar Hamas wadda ta fitar da gargadin ko dai Isra'ilan ta gaggauta janye dakarunta ko kuma ta karbi rikicin, kamar yadda kusa a kungiyar Isma'il Haniya ke fadi: "Ba za mu lamunci ci gaba da yin kutsen 'yan mamaya cikin Masallacin Al-aqsa ba. A shirye muke mu sadaukar da rayukanmu domin hana afkuwar hakan. Za mu ci gaba da harbawa Isra'il rokokinm mu kuma ci gaba da fafata wa har sai mun 'yanta dukkan Masallacin Al-aqsa da birnin Kudus.

Karin Bayani: Martanin ƙasashen duniya a kan Isra'ila

A hannu guda kuma, Isra'ila ta sanya dokar ta-baci a birnin Lod, bayan boren da Larabawa mazauna Isra'ila suka yi na nuna adawa da korar Falasdinawan unguwar Sheikh Jarrar da ke Kudus, domin bai wa Yahudawa 'yan mammaya gidajensu. An cinnawa motoci wuta kuma wani mutum da 'yarsa - dukkkansu Larabawan Isra'ila sun mutu lokacin da wani makamin roka ya fada kan motarsu. Wannan dai shi ne bore mafi muni da aka yi a yankin tun 'yan shekaru.

Marokko Demonstration gegen den Nahost-Plan von US-Präsident Trump
Al'ummar Muslsumi na zanga-zangar adawa da mamayar Isra'ila a FalasdinuHoto: picture-alliance/AA/J. Morchidi

Kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya watse daga taron da ya yi kan batun ba tare da ya yi wani jawabin karshe ba. Koda yake kakakin sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar, Stéphane Dujarric yin tir ga Isra'ilan kan keta hurumin Al-Aksa da kokarin raba Falasdinawa da gidajensu karfi da yaji a birnin Kudus ke karade kasashen Musulmi, ciki har da kasashen da a 'yan kwanakin baya-bayan nan suka kulla hulda da Isra'ilan. Hatta limamin harami duk da sabuwar dokar da ke hana su tsinewa Yahudawa da Bin Salman ya kafa, a wannan karon zuciya ta kwashe shi, inda ya dira kan Isra'ilan da yi mata mummunar addu'a.