1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar da Burkina za su yaki ta'addanci

Gazali Abdou Tasawa
September 11, 2022

A karon farko shugaban gwamnatin mulkin soji na Burkina Faso Paul-Henri Sandaogo Damiba ya gana da takwaransa na Nijar Mohamed Bazoum kan batun yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4Gh2E
Burkina Faso | Militärleiter Paul-Henri Sandaogo Damiba
Hoto: Radiodiffusion TÈlÈvision du Burkina/AFP

Kasashen Nijar da Burkina Faso sun jaddada aniyarsu ta kara hada kai a tsakaninsu domin yakar 'yan ta'adda a iyakokinsu. Shugaban mulkin rikon kwarya na Burkina Faso Paul-Henry Sandaogo Damiba ya bayyana hakan a ziyarar da ya kai a wannan Lahadi a birnin Niamey bayan da ya gana da shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Damiba ya ce: ""kun san matsalar tsaro a iyakokin kasashenmu uku na ci gaba da daukar mana da hankali. Wannan dalili ne ya sa na yi tafiyayya zuwa Nijar domin tattaunawa da shugaban kasar ta Nijar kan hanyoyin da ya kamata mu tinkari wannan kalubale na tsaro da zummar samar da sabin dabaru na tunkararta da karfi".

Shugaban Burkina Faso ya kai ziyarar ne kwanaki kalılan bayan wata mai kama da ita da ya kai a kasar Mali a kokarin da kasashen uku ke yi na ganin Mali wacce ta face daga hadakar G5 Sahel mai yaki da ta'addanci ta dawo an ci gaba da damawa da ita.