Al'amura sun fara kankama gabannin harkokin zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar, inda 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki kan zaben ke cigaba caccakar juna.
https://p.dw.com/p/1GB6X
Talla
'Yan siyasa da hukumomin da ke da ruwa da tsaki kan zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Nijar sun fara shirin zabe wanda za a gudanar cikin shekara mai kamawa. Sauran al'ummar gari da masana harkokin siyasa kuwa tsokaci suka fara yi kan batun.