1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin haske kan takunkumin kan China

Zulaiha Abubakar
May 29, 2018

Fadar mulki Amirka ta White House ta bayyana cewar takunkumin cinikayyar da ta kakabawa kasar China na nan daram nan bada jimawa kuma da za ta sanar da wasu sabbin bayanai a kan lamarin.

https://p.dw.com/p/2yYoC
Symbolbild zur drohenden Zuspitzung des Handelskrieg s zwischen den Vereinigten Staaten von Amerika
Hoto: imago/R. Peters

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da sakataren cinikin Amirka Wilbur Ross ke dab da kai ziyara kasar ta China don bude wata sabuwar tattaunawar kan hanyoyin warware rikicin cinikayyar da ya balle tsakanin kasashen biyu bayan China ta fara yi wa Amirka barazanar sanya takunkumi a kan dukkan kayan da aka shigo dasu daga kasar. Da ta ke karin haske hukumar ciniki ta kasar China ta shawarci kasar ta Amirka da ta mutunta sharadan da kasashen biyu suka amince tun da farko.