1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron rage dumamar duniya

Binta Aliyu Zurmi
October 31, 2021

Shugaban taron kolin Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi COP26 ya baiyana taron Glasgow a matsayin dama ta karshe ta rage dumamar duniya.

https://p.dw.com/p/42Pcz
COP26  | Alok Sharma
Hoto: Alberto Pezzali/Pool/AP/picture alliance

Shugaban babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi karo na 26 da aka yiwa lakabi da COP26, Alok Sharma ya baiyana taron Glasgow kan sauyin yanayin da cewa ita ce dama ta karshe ta rage dumamar duniya da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius.

Da yake bude taron a yau Lahadi Alok Sharma ya yi tsokaci kan mummunan tasirin da gurbataccen hayakin masana'antu ya yi ga dumamar duniya tsawon shekaru 150 da suka gabata.

Kwararrun masana muhalli sun yi gargadin cewa daukar managarcin mataki cikin shekaru goma masu zuwa shi ne kadai zai sauya tasirin illar da ake fuskanta daga dumamar yanayi a halin yanzu.

A nasa bangaren Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bukaci shugabannin duniya dake halartar taron su nuna kwakkwaran kudiri na shawo kan dumamar duniyar idan ana so a cigaba.