Dalilan Merkel na ziyartar PM din Canada
August 16, 2012Talla
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta isa birnin Ottawa na Canada domin tattaunawa da firaminista Stephen Harper, game da rikicin kudi na Turai da yarjejeniyar cinikayya tsakanin kasar da kuma takwarorinta na Eu. Ita dai kasar ta Canada ta na daga cikin jerin manyan kasashen duniya da ba su taimaka wa kasashen Turai ceto kansu daga kangin tattalin arziki da suka shiga ba.
Tuni ma dai gwamnatin ta Ottawa da jadadda matsayinta na kin bayar da ko da sisin kwabo ga kasashen na Turai domin taimaka ma tattalin arzikin tsayawa akan kafafunsu. Biyar daga cikin 'yan kasuwan Jamus da za su yi musayyar bayanai da takwarorinsu na Canada ne ke rufa wa Merkel baya a wannan ziyara ta kwanaki biyu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu