1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan na sake shiga tasku

August 11, 2021

Kasashen Jamus da Netherlands sun sanar da dakatar da mayar da 'yan Afghanistan da ke neman mafaka gida.

https://p.dw.com/p/3yqsC
Afghanistan abgeschobene Asylbewerber kehren zurück
Tuni dai Jamus din ta mayar da wasu masu neman mafakar zuwa gida AfghanistanHoto: Getty Images/AFP/W. Kohsar

Kamfanin dillancin labaran Jamus din dpa ya ruwaito ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamus din na bayyana da cewa, sakamakon halin rashin tabbas kan tsaro da a yanzu haka Afghanistan din ke ciki, mahukuntan Berlin sun yanke shawarar dakatar da mayar da masu neman mafakar na Kabul zuwa wani lokaci. Tun bayan da dakarun sojojin kasashen ketare suka fara ficewa daga Afghanistan din ne dai, mayakan na Taliban suka fara zafafa hare-hare tare da kwace iko da yankuna da dama a kasar. Ita ma kasar Netherlands, ta sanar da dakatar da mayar da masu neman mafaka daga Afghanistan din gida. Kawo yanzu mayakan na Taliban, sun kwace iko da manyan biranen gundumomi tara cikin 34 da ake da su a Afghanistan din.