1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Somaliya sun kwace ikon Haradhere

January 16, 2023

Dakarun Sojan Somaliya sun sanar da kwace ikon wani mihimmin gari, wanda fiye da shekaru 10 yake karkashin ikon mayakan Al-Shabaab.

https://p.dw.com/p/4MHHN
Mayakan Al-Shabaab
Hoto: picture alliance / AP Photo

Bayan garin ya shafe tsawon shekaru 10 karkashin ikon mayakan kungiyar Al-Shabaab, dakarun Somaliya sun samu nasarar kwace ikon garin Haradhere. Mataimakin ministan sadarwa na kasar Hussein Ahmed ya ce, garin na Haradhere da ke da nisan kilomita 500 daga babban birnin kasar Mogadishu ya kasance babbar hanyar da mayakan ke amfani da ita wajen sintiri.

Ahmed ya kara da cewa, nasarar kwace iko da garin da dakarun Somaliyan suka yi ta kasance babbar nasara a cikin tarihi ga 'yan kasar. Ya ce shekarar 2023 za ta kasance shekara ta 'yanci da za a kakkabe mayakan na Al-Shabaab. Kasar Somaliya dai ta kwashe tsawon kimanin shekaru 15 ta na fama da matsalolin mayakan, inda suke kai hare-hare a kasar da ma makwaftanta.