1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun siriya sun sake kai hari a ƙauyukan da ke kusa da Turkiyya

September 5, 2011

Al'ummar Siriya ta fara kauracewa zuwa kasashen da ke makobtaka da ita

https://p.dw.com/p/12TQr
Hoto: picture alliance/dpa

Dakarun Siriya sun hallaka wani farin hula a lokacin wani samamen da suka kai waɗansu ƙauyuka da ke kusa da Turkiyya. Shaidu sun bayyanawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa dakarun sun harbe Abdulsalam Hassoun, wani maƙeri mai shekaru 24 da haihuwa bayan da ya ƙetara zuwa Turkiyya daga ƙauyen Ain al-Baida dake Siriyan.

Masu fafutukar kare haƙƙin jama'a a ƙauyukan sun ce dakarun sun kai samamen ne domin hana fararen hula tsallakawa zuwa Turkiyyan don neman mafaka sakamakon irin danniyar da suke fuskanta. Wannan ne samame mafi girma a yankunan da ke kan iyakan tun a watan Yunin da ya gabata, lokacin da ɗaruruwan mutane suka ƙauracewa matsugunnensu.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Abdullahi Tanko Bala