1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya na yunkurin kwance damarar 'yan tawaye

March 19, 2012

A daidai lokacin da tawagar da Kofi Annan ya aika ta isa Siriya, dakarun gwamnati sun sake kai sabbin hare-hare a yankunan 'yan tawaye

https://p.dw.com/p/14Mrn
In this image made from amateur video released by DPN (Deir el-Zour Press news) and accessed via The Associated Press Television News on Wednesday Aug. 10, 2011, shows Syria tanks on the street in Deir el-Zour Syria on Tuesday Aug. 9. 2011. Syrian troops seized control of the eastern flashpoint city of Deir el-Zour Wednesday following intense shelling and gunfire, an activist said, as the international community intensified its pressure on the country's president to end the deadly crackdown. (Foto:DPN via APTN/AP/dapd) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL
Hoto: dapd

Manyan tankokin yakin dakarun Siriya da dama ne suka kutsa zuwa birinin Dair al-zour inda mafi yawan al'ummarsa 'yan sunni ne, a wani sabon yunkuri na neman anshe mahimman yankunan da ke karkashin jagorancin dakarun 'yan tawayen masu zaman kansu wadanda ke cigaba da kara himma wajen kai hari kan dakarun gwamnati, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Tankoki da motocin yakin masu sulke sun shiga birnin daga arewaci inda 'yan tawayen suka rika nuna turjiyayi a yayin da suke janyewa zuwa ungwanin da ke kudu maso gabashin birnin wadanda ke zaman inda dakarun nasu suka fi karfi.

A yayinda hakan ke faruwa a waje guda kuma wata tawaga ta musamman da manzon hadin gwuiwa na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadin Kan Larabawa a rikicin Siriyar, Kofi Anan ya aika kasar ta isa, kuma zata kasasnce a Siriyar har sai sadda aka fara samun ci-gaba wajen ayyukan da zasu kawo karshen zud da jinin da ke gudana ba kakkautawa.

Ahmad Fawzi wanda yayi magana a madadin Kofi Anan, ya fadawa kamfanin dillancin labarun Faransa na AFP cewa ba zai iya fayyace cikakken shirin da tawagar zata aiwatar a Siriyar ba kuma ziyarar da Anan zai sake kaiwa ya dogara ne a kan cigaban da aka samu daga ayyukan 'yan Siriyar da na tawagar da ta isa yanzu.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Abdullahi Tanko Bala