1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Siriya na ci gaba da murƙushe masu bore

Holly FoxOctober 8, 2011

Amirka ta sake yin kira ga shugaba Bashar al-Assad na Siriya da ya sauka cikin girma da arziƙi.

https://p.dw.com/p/12oBJ
Masu bore a birnin Homs na SiriyaHoto: dapd

Gwamnatin shugaba Barack Obama na Amirka a ranar Juma'a ta yi kira ga shugaba Bashar al-Assad na Siriya da ya sauka daga kan karagar mulki nan ba da daɗewa ba. A wata sanarwar da ta fitar kakakin fadar gwamnatin ta White House, Jay Carney ya yi Allah wadai da kisan jagoran Kurdawa masu adawa Meshaal Tamo, kuma ta ce Assad na ƙoƙarin jefa ƙasar cikin wani mawuyacin hali. Masu Fafutukar kare haƙƙin bil adama sun ce ko a ranar Juma'an dakarun gwamnati sun hallaka wasu masu bore guda 15. Wannan tashin hankali na zuwa ne kwanaki ukku bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kasa zartar da ƙudurin da zai yi barazanar sanya wa Siriyar takunkumi idan har ba ta daina kai hari kan fararen hula ba. Ƙasashen Rasha da China ne suka hau kujerar na-ƙi dangane da wannan batu. Kawo yanzu Majalisar Ɗinkin Duniyar tana kiyasin cewa kimanin mutane 2,700 suka mutu tun bayan da gwamnatin Assad ta fara murƙushe masu boren da ke kiransa da ya sauka daga kujerar mulkin ƙasar.

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Halima Balaraba Abbas