1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Rasha sun janye daga Lyman

October 1, 2022

Dakarun Rasha sun janye daga garin Lyman da ke gabashin Ukraine, bayan da Rasha ta yi fargabar cewa, daruruwan dakarunta ka iya fadawa tarkon dakarun Ukraine.

https://p.dw.com/p/4Hde6
Ukraine I Beschuss in der Nähe des Bahnhofs in Lyman
Hoto: Yashuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Dakarun Rasha sun tabbatar da janyewa daga garin Lyman na yankin Donesk da ke gabashin Ukraine. Hakan na zuwa ne bayan da Rasha ta yi fargabar cewa, dakarunta kimanin dubu biyar ka iya fadawa tarkon dakarun Ukraine.

A wannan Asabar din ce dai Ukraine ta sanar da yiwa garin kawanya tare da kwace ikon Lyman din, bayan dauki ba dadi da ake yi tsakanin bangarorin biyu da ke yaki.

A makwannin baya-bayan nan dai Rashar ta fuskanci koma bayan ayyukan soji a yakin da take yi da makwafciyarta. Ko da yake a ranar Juma'a, Rashar ta yi bikin shigar da yankuna hudu na Ukraine cikin kasarta; sai dai kuma shugaba Volodmyr Zelensky ya sha alwashin cewa dakarun Kiev za su sake kwato yankunan.