1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Kudancin Sudan sun kashe farar 'hula bisa kuskure

December 27, 2011

Gwamnatin ta nemi ahuwa akan abinda ta kira na ɓacin rai bayan da sojojin kasar suka bindige wasu mutane gud fuɗu

https://p.dw.com/p/13aNC
An SPLM-N fighter sits on a camouflaged truck at the bush camp of the rebel movement’s leader, Malik Agar. Copyright: Jared Ferrie, DW freier Mitarbeiter, Kurmuk, Sudan October 2011
Sojin Kudancin SudanHoto: DW

Wani kakakin rundunar sojoji kudancin Sudan Philip Aguer ya sanar da cewar dakarun ƙasar sun kashe wasu ma'abiya addinin krista guda fuɗu kana kuma suka raunata wasu guda 15 bisa kuskure,a kusa da wata coci a lokacin da aka gudanar da bukukuwan sallah krismetri a garin Piji da ke cikin jihar Jonglei.

Kakakin ya ce saojojin sun buɗe wuta ne kan mai uwa da wabi a sa'ilin da suka tsintsi gawar wani sojin gwamnatin wanda aka kashe da harbin bindiga a kusa da cocin.ya kuma ce yanzu haka ana tsare da labtanan sojin da ke jagorantar bataliyar sojojijn wacce ke yin sinitiri a lokaci faruwa lamarin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammed Nasiru Awal