1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Amirka na janye tankokin yaki a Iraki

Abdul-raheem Hassan
February 5, 2018

Sojojin Amirka da suka fafata da mayakan IS, sun fara ficewa daga kasar bayan cimma nasarar murkushe kungiyar da ta mamaye wasu manyan cibiyoyin kasar.

https://p.dw.com/p/2s9Dt
Irak Offensive auf IS-Hochburg Hawidscha
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye

Kakakin gwamnatin Iraki Saad al-Hadithi ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarun AP cewa an fara samun raguwar adadin dakarun Amirka da ke jibge a kasar.

Wata majiya daga cibiyar rundunar sojojin ta ce an fara kaurar da manya-manyan kayan yaki da suka hada da tanokin yaki daga Iraki zuwa Afganistan.

Gwamnatin Bagadaza ta ce wannan shi ne karon farko cikin shekaru uku da aka cimma yarjejeniyar rage adadin sojojin Amirka a Iraki, tun bayan da Amirka ta sa kafar wando da kungiyar IS inda ta kaddamar da somamen farko a shekarar 2014.