Dage dokar ta baci a Siriya
April 21, 2011Talla
Gidan telebijan kasar Siriya ya ba da rahoton da ke nuni da cewa Shugaba Bashar Al-Assad ya ba da umarnin dakatar da dokar ta-baci da aka gindaya kusan shekaru hamsin da suka gabata-matakin da za rusa kotuna na musamman ya kuma ba al'uma damar gudanar da zanga-zanga a cikin limana. Akalla mutane 21 suka rasa rayukansu a wannan mako bayan da aka gudanar da zanga-zangar samar da walwalar siyasa da kuma yin kira ga shugaba Assad da ya yi murabus. A dai halin da ake ciki yanzu an baza dakarun sintiri masu saye da rigunan farar hula dauke da bindigogin AK 47 domin kamen 'yan zanga zanga.
Mawallafiya Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal