1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Huldar Italiya da Faransa na nan ba sauyi

Yusuf Bala Nayaya
January 22, 2019

Italiya dai ta zargi kasar Faransa da haifar da talauci a Afirka lamarin da ya haifar da tarin 'yan gudun hijira zuwa Turai. Lamarin da ya jawo nuna wa juna yatsa.

https://p.dw.com/p/3BzZm
Italien Giuseppe Conte, Premierminister in Rom
Firaminista Giuseppe Conte na ItaliyaHoto: Reuters/A. Bianchi

Dangantaka tsakanin Italiya da Faransa na nan yadda aka santa a matsayin kawayen juna duk kuwa da takaddama da ke wakana tsakanin kasashen biyu kan batun 'yan gudun hijira. Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya bayyana haka a wannan Talata a kokari na yayyafa ruwan sanyi a musayar zafafan kalamai da ake yi tsakanin mahukuntan na biranen Rome da Paris.

A ranar Litinin ce dai Faransa ta nemi jakadanta a kasar ta Italiya ya koma gida bayan da mataimakin firamanistan kasar ta Italiya Luigi Di Maio ya zargi mahukuntan Paris da haifar da yanayi na talauci a kasashen Afirka. Abokin aikinsa ma Matteo Salvini ya bi sahunsa inda ya zargi Faransa da rashin tabuka komai wajen maido da zaman lafiya a kasar Libiya.