1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dagantakar Birtaniya da Isra'ila ta yi tsami

March 23, 2010

A dai dai lokacinda dangantakar Isra'ila da Birtaniya ke ƙara tsami, ƙasar Birtaniya ta kori wani jami'in dipalmasiyar Isra'ila

https://p.dw.com/p/MaLq
Gordon Brown

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Milliban ya bada umarnin a tisa ƙiyar wani jami'in dipalmasiyar Isra'ila dake Birtaniya, bayan zargin da aka yi na cewa wasu yan Isra'ila 12, sun yi anfani da fasfunan Birtaniya na jabu, inda suka hallaka wani ɗan ƙungiyar Hamas a birnin Dubai cikin watan janairu. Da yake jawabi a majalisar dokokin ƙasar, Milliban yace akwai ƙwararan shaidu, dake nuna hannun Isra'ila wajen samar da fasunan bogi, da sunan Birtaniya. "YAce sabo da haka gwamnati tana ɗaukar matakai bisa shaidun da muka samu a wannan lamarin, domin mubayyana rashin jin daɗinmu, kuma ne samun tabbacin cewa hakan bazai sake faruwa ba" Milliban yace hakan ya karya ƙa'idar amanar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman.

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal.