1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Covid-19: Yunwa a gidajen namun dajin Uganda

April 23, 2020

Ana fargabar dabbobin da ke  gidajen namun daji a kasar Uganda za su shiga cikin garari saboda Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3bJtN
Deutschland | Löwenfütterung im Zoo Duisburg
Hoto: picture-alliance/dpaR. Weihrauch

A shekarar 2019 mutum 385,000 suka ziyarci gidan kallon dabbobin kasar amma kuma a wannan shekarar tun daga watan Janairu mutane suka fara nesa-nesa da wurin, saboda dokokin takaita yaduwar Covid-19. Lamarin dai ya rage kudin da ake samu daga 'yan kallo don ciyar da dabbobin da ke kulle a gidan. 

Gidajen adana dabbobi na duniya dai na ci gaba da dandana tasirin annobar Coronavirus, inda wani gidan zoo a Jamus shi kuma yayi kurarin idan har ya ci gaba da fuskantar rashin kudi to zai iya barin dabbobi su ci 'yan uwansu a saboda rashin kudin ciyar da su.