1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSudan

Cutar kwalara ta sake kunno kai a Sudan mai fama da yaki

Mouhamadou Awal Balarabe
August 23, 2024

A karo na biyu cikin watanni shida, cutar amai da gudawa ta barke a Sudan a daidai lokacin da kasar ke fama da yaki. WHO ta kai daukin alluran rigakafi don taimaka ma wadanda suka kamu ita.

https://p.dw.com/p/4jqXk
Yaran da suka kamu da kwalara na samun kulawa a garin Wad Al-Hilu na Sudan
Yaran da suka kamu da kwalara na samun kulawa a garin Wad Al-Hilu na SudanHoto: AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta samar da karin alluran rigakafin kwalara 455,000 a Sudan domin taimaka wa kasar tunkarar sabuwar annobar amai da gudawa da ta barke. A ranar 12 ga watan Agusta ne  kwalara ta sake konno kai a Sudan  bayan kawo karshen bullar ta a watan Mayun da ya gabata, inda fiye da mutane 11,300 suka kamu da kwalara yayin da fiye da 300 suka mutu.

Karin bayani: Me ya sa cutar kwalara ke karuwa a duniya?

 WHO ta ce a halin yanzu, sabuwar  kwalarada ke haddasa annobar ta amai da gudawa ta kama mutan 658 yayin da mutane 28 suka mutu a jihohi 5 da suka hada da Kassala da Gedaref da al-Jazeera, da Khartum. Sai dai yakin da ake gwabzawa tsakanin sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhane da dakarun Janar Mohamed Hamdane Daglo na kawo cikas wajen kai magunguna da sauran kayan agaji ga mabukata.