1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kinshasa: Gidajen yari sun cika makil

September 18, 2024

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun yi tir da cunkoson gidajen yari a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar mutane 129 a gidan yarin Makala da ke birnin Kinshasa.

https://p.dw.com/p/4klR8
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango I Gidan Yari | Makala | Beni | Cunkoso
Gidajen yarin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, cikin halin cunkosoHoto: John Kanyunyu/DW

Ko da a gidan yarin Beni da ke lardin Kivu ta Arewa a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, yanayin rayuwar fursunonin na haddasa damuwa saboda karancin abinci da matsalolin ruwa da kiwon lafiya. Kimanin fursunoni 1,500 ne suke tsare a dakuna da aka ware musu a gidan gyaran hali na Kangbayi da ke Beni, alhali an gina shi domin daukar mutane 250 kawai. Wannan cunkoso ne ya sa aka tsugunar da fursononi mata da yara, a wasu gine-gine na wani yanki na birnin. Wani tsohon fursuna wanda ya nemi a sakaye sunansa da ya yi watanni uku a gidan yarin Kangbayi, ya danganta shi da wani dandali na mutuwa salamu alaikum. Baya ga tallafin abinci da gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke bayarwa, hukumomin gidan gyaran hali na Beni na samun gudunmawar da coci-coci da sauran masu hannu da shuni. Amma acewar tsohon fursunan abinci ba ya isar fursunoni, saboda haka ya kamata a saka su cikin aikin noma ko wani aiki dabam da zai taimake su wajen samun kudin shiga domin samun na sawa a baka.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango I Gidan Yari | Makala | Beni | Cunkoso
Tashin hankali a gidajen yarin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, saboda cunkosoHoto: Jean Noel Ba Mweze/DW

A tsakiyar watan Agusta, gabanin tashin hankalin da ya faru kuma ya salwantar da rayuka a gidan gyaran hali na Makala da ke Kinshasa, Ofishin Hadin Gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya ya kiyasta mutuwar mutane 238 a gidajen yarin Kwango tun farkon wannan shekara ta 2024. Lauya Elie Kiyonga da ke fafutukar kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya bayyana yarin kasar a matsayin wurin da ake danne hakkin fursunoni. Jami'an gidan gyaran hali na Beni sun hana ma'aikatan DW shiga gidan yarin, kuma sun ki amsa tambayoyin da muka aika musu. Amma idan za a iya tunawa a ranar 20 ga Oktoban 2020 an kai hari a gidan gyaran hali na  Beni da sanyin safiya, wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa a kasar ta Tsakiyar Afrika. A cewar hukumomin Kwango kimanin fursunoni 1,300 ne suka tsere a ranar, kuma yawancinsu manyan masu laifi ne da ke jiran shari'a. Amma har yanzu ba a fayyace yanayin tserewar fursunonin ba, sai dai an gina katanga a kewayen gidan yarin domin inganta tsaro da hana fursononi arcewa.