1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

COVID-19: Trump ya ce za a samar da rigakafi

May 4, 2020

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce yana da kwarin gwiwar Amirka za ta samar da rigakafin cutar COVID-19 a karshen bana daidai lokacin da yake bude tattalin arzikin kasar.

https://p.dw.com/p/3bjZ5
USA | Washington | Donald Trump während einer Fernsehaufzeichnung mit dem US-Sender Fox News im Lincoln Memorial
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/E. Vucci

Shugaba Donald Trump dai na fadin hakan ne musamman lokacin da yake amsa tambayoyi daga masu zabe da kafar talabijin ta Fox News ta watsa. Kwararru dai na cewa samar da rigakafi abu ne da ke daukar lokaci.

Shi ma kwararre kan cutuka masu yaduwa a Amirkar Anthony Fauci, ya ce ta yiwu rigakifin ya samu cikin watan Janairu, sai dai babu tabbas.

Ministan lafiya na kasar Jamus kuwa, Jens Spahn a nashi bangaren cewa ya yi hada allurar rigakafi shi ne abu mafi wahala a aikin harhada magunguna, abin da ya ce ke iya kai kwararru tsawon shekaru.