1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damar yin Sallar Idi a gida saboda COVID-19

Yaya Azare Mahamud LMJ
May 19, 2020

Cibiyar binciken addinin Musulumci ta al-Azhar da majalisar malaman Saudiyya, sun bai wa Musulmin da cutar corona da ta tilasta musu yin kulle damar yin Sallar Idi a cikin gidaje tare da iyalansu koma su kadai.

https://p.dw.com/p/3cUFq
Ahmed Al Tayeb sheikh
Babban limamin cibiyar al-Azhar Ahmed Al Tayeb sheikhHoto: picture-alliance/Catholic Press Photo

Shugaban Majalisar Malamai ta Saudiyya kuma babban mai fatawa, Sheikh Abdul Aziz Al-Asheikh ya ce, ya halatta mutane su yi Sallar Idi a gidajensu a irin wannan lokaci na annobar coronavirus. Ya kara da cewa za a iya yin sallar ba tare da huduba ba. Galibin malamai dai na daukar hukuncin Sallar Idin a matsayin sunnah, koda yake Ibn Taymiyya na daukar sallar a matsayin farillar da dole a rama idan ta kufcewa mutum, kamar yadda sheikh Abdallah Mudallaq mamba a majalisar fatawar ta Saudiyya ya tabbatar.

Ya ake Sallar Idi?

Shi kuwa Sheikh Abdul Azeez bin Duneet wani mamba a kwamitin fatawar na Saudiyya, cewa ya yi Sallar Idin sunnace da a ka karfafi yin ta, don haka ba dole ba ne a rama idan ta kubce, koda yake ya ce manyan bayin Allah da suka gabata suna kokarin ramata idan ta kubce musu, su kadai ko tare da iyalansu.

Nigeria Frauen machen einen Selfie
Iyalai su yi Sallar Idi a gidaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

To sai dai kamar  yadda Sheikh Labeeb Nageeb na cibiyar Al-Azhar ke cewa, akwai malaman da suke ganin za a iya yin huduba ko da kuwa da karanta abin da ya sauwaka daga cikin al-Kur'ani mai girma a yayin Sallar Idin a gida.Lokacin Sallar Idi dai ya kan fara ne daga lokacin Sallar Walaha, wato bayan gama hudowar rana har zuwa kusan tsakiyar rana kafin zawali. Kuma ta kunshi raka'a biyu tare da kabbara shida a raka'ar farko bayan kabbarar harama, sannan a yi kabbara biyar a raka'a ta biyu, bayan kabbarar tasowa daga sujjada.

Kabbara ta fi ziyara

Wasu malaman sun ce anso a karanta Suratul A'ala a raka'ar farko sai kuma Gashiya a raka'a ta biyu. Kamar yadda ake son sanya sababbin tufafi da fesa turare da kuma yalwata iyali da abinci, hada da ziyarce-ziyarcen dangi da 'yan uwa da makwabta, wanda a wannan karon maluman addini da mahukunta suka nemi da a kaurace musu. Sheikh Ateef Alee na jam'iar Al-Azhar ya nunar da cewa, yawan kabbara daga cikin gidaje zai wadatar ba sai an yi ziyarci juna ba a wannan karon.