1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta shawo kan annobar Corona

Ramatu Garba Baba
September 14, 2020

A karon farko gwamnatin kasar Masar ta amince da bukatun jama'a na gudanar da shagulgulan biki da taron mutanen da ba zai haura mutum dari uku ba a kokarinta na hana yaduwar cutar Corona.

https://p.dw.com/p/3iT24
Coronavirus | Hochzeit | Liebe | Paar | Ägypten | Kairo
Hoto: Reuters/R. Gomaa

Kasar Masar ta kasance kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta dage dokar hana tarukan jama'a tun bayan bullar annobar Coronavirus a nahiyar a hukumance, daga dai ranar ashirin da daya ga wannan watan na Satumbar da muke ciki, jama'a na da damar gudanar da taron bikin aure dama wasu taruka na nishadi da jama'a ba su zarce dari uku ba.

Watanni da dama kenan da gwamnatin kasar ta ayyana dokar haramta duk wani taron jama'a a kokarinta na hana yaduwar cutar da ta riga ta halaka mutum sama da dubu biyar a sassan kasar. Amma an sami raguwar alkaluman masu kamuwa da cutar a 'yan kwanakin nan.