1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Akwai bukatar ci gaba da dokar hana yaduwar Corona

Ramatu Garba Baba
May 27, 2020

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana bukatar kara yin taka tsantsana a yakar cutar Coronavirus duk da kiran da gwamnonin jihohin kasar suke yi na a sassauta dokar don bai wa jama'a 'yancin walwala.

https://p.dw.com/p/3crjH
Deutschland Angela Merkel
Hoto: picture-alliance/AP Photo:M. Kappeler

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce, akwai bukatar a kara yin taka tsantsana a yakin da ake da cutar numfashi ta Coronavirus, batun da ke zuwa bayan da gwamnonin wasu jihohin kasar suka bukaci a sassauta dokar don bai wa jama'a 'yancin walwala. A ganawar da ta yi da su ta kafar bidiyo, Merkel ta ce zai yi wuya a janye dokar amfanin da kyalen rufe fuska da sa tazara a tsakanin jama'a ganin har yanzu ba a gano riga-kafi dama maganin cutar ba. Jamus dai na shirin janye dokar hana zirga-zirga a tsakanin kasashen Turai daga ranar sha biyar ga watan Yuni mai zuwa.

Daga ranar talatin ga watan Mayu, al'ummar Poland  da ke makwabtaka da Jamus, za su soma fita ba tare da sanya kyalen rufe fuska ba, hakazalika za a bude gidajen kallo da wuraren motsa jiki daga ranar shida ga wata mai kamawa, alamu sun nuna kasar ta yi nasara a yakar cutar ta Covid-19. Hakazalika kasar Switzerland za ta bude iyakokinta amma banda ta kasar Italiya za a kuma soma barin jama'a su gudanar da taro.

Ma'aikata sama da miliyan dari uku ne zasu rasa aikin yi a sassan duniya a sakamakon annobar Coronavirus, kiddidigan ya hada daga watan Afrilu ya zuwa Yuni kamar yadda kungiyar kwadago ta duniya ta sanar a wannan Laraba.

Wannan na zuwa ne a yayin da cutar ke ci gaba da yaduwa a Amirka, a jihohi ashirin aka tabbatar da sabbin alkaluma na wadanda suka kamu da cutar, mutum kusan dubu dari cutar ta halaka a kasar. A Kasar Mexico da ke yankin Latin Amirka ma, yawan wadanda cutar ta kashe a kwana guda ya zarta dari biyar, wanda shi ne mafi girma tun bayan bullar cutar a kasar.

A nahiyar Turai kuwa, Faransa da Italiya da kuma Beljiyum sun dauki matakai na dakatar da amfani da maganin hydroxychloroquine kan masu fama da Coronavirus bayan da aka diga ayar tambaya kan sahihancin maganin da a abaya can ake amfani da shi wajen warkar da zazzabin Malariya.

Yan kasar Malawi fiye da dari hudu da aka mayar kasar daga Afrika ta Kudu ne suka tsere daga wani wuri da ake kebe wadanda ake zargin na dauke da cutar Coronavirus, cikinsu har da wasu da aka riga aka tabbatar na dauke da cutar. Gift Kawaladzira, wani jami'in kiwon lafiya ne da ya tabbatar da labarin batan dabon da mutanen suka yi, inda ya ce tuni aka tura jami'an tsaro farautarsu.