1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Trump ya ce ana samun nasara

July 3, 2020

Shugaba Donald Trump na Amirka, ya sake yaba yadda gwajin cutar corona ke tafiya a kasar, daidai lokacin da wadanda suka kamu a ranar Alhamis ya zarta dubu 55 a Amirkar.

https://p.dw.com/p/3ej4t
US Präsident Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm

Karuwar samun wadanda ke kamuwa da cutar a makon da ya gabata, ta sanya mutane sa ido sosai kan yadda Mr. Trump ke yi wa lamarin riko a kasar.

Su ma gwamanonin wasu jihohin kasar sun yanke shawarar dakatar da shirinsu na sake bude harkoki bayan tsauraran matakan da suka dauka na kulle a jihohin nasu.

Shugaba Trump ya yi kurarin cewa duk da kasancewa ana samun karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19, aikin gwaji dai na tafiya, sannan alkaluman wadanda ke mutuwa kulli yaumin dai na raguwa.