1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adadin wadanda suka mutu da Coronavirus sun karu a duniya

Abdoulaye Mamane Amadou
April 16, 2020

Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa cutar Coronavirus a duniya ya haura dubu 137 kamar yadda wata kididdiga da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya fitar.

https://p.dw.com/p/3b06b
Coronavirus Brasilien Porto Alegre Intensivstation für Covid-19 Patienten
Hoto: AFP/S. Avila

Kididdigar ta ce har ya zuwa  yau da misalin karfe 11 na safe fiye da mutun milliyan 2. 083.820 ne sabbin kamuwa da cutar a kasashe193 tun bayyanar annobar a duniya. Amirka ita ce ke kan gaba da mamata dubu 30 da 985 daga cikin mutane dubu fiye da dubu 639 dfa suka kamu da cutar. Italiya ita ce ta biyu da mamata dubu 21 da 645, sai kasar Spain mai mutane dubu 19 da 130, Faransa na bioye mata da mamata dubui 17 da 167 daga karshe sai kasar Birtaniya wacce ta kiddige mamatanta da suka kai dubu 12 da 868 daga cikin mutn fiye da dubu 98 da suka kamu da cutar.

Kididdigar ta kamfanin AFP ta ce a nahiyar Afirka mutun 910 ne suka mutu sakamakon cutar, daga cikin dubu 17 293 da suka harbu da ita.