1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin duniya na fuskantar barazanar

June 10, 2020

Rahoton kungiyar kawance raya ci gaban tattalin arzikin nahiyar Turai ta OECD ya ce tattalin arzikin kasashen tarayyar Turai zai samu yi nakasu da kashi shidda cikin dari sanadiyar annobar Covid-19.

https://p.dw.com/p/3dZyx
Frankreich OECD Treffen in Paris | Generalsekretär Angel Gurria
Hoto: Getty Images/AFP/E. Piermont

A cewar karfin tattalin arziki a kasashe 37 na kungiyar ya durkushe sanadiyar bullar annobar ta Corona. Kungiyar kawancen raya ci gaban tattalin arziki a nahiyar Turai wato OECD ta ce, tattalin arzikin duniya zai ragu da kaso shida cikin dari a bana, sakamakon halin da aka shiga na annobar Corona. 

OECD ta kara da cewa kasashe da dama na duniya za su fuskanci karancin kudin shiga da kuma halin rashin tabbas na koma bayan tattalin arziki. Bayanin kungiyar dai ya ce idan aka kara samun barkewar annobar karo na biyu, tabbas tattalin arzikin na duniya zai fadi kasa warwas da kaso bakwai da digo shida cikin dari.