1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona: Mutane sun yi zanga-zanga a Jamus

Ahmed Salisu
September 12, 2020

Kimanin mutane dubu goma ne a birnin Munich na jihar Bavaria da ke Jamus suka gudanar da wata zanga-zanga ta kin jinin matakan kariya da hukumomi ke cigaba da amfani da su wajen yaki da annobar corona.

https://p.dw.com/p/3iOAV
Deutschland | Protest gegen Corona-Maßnahmen in München
Hoto: picture-alliance/dpa/V. Gensch

Gabannin gudanar da zanga-zangar, hukumomi sun sanar da hanata amma daga bisani wata kotu da sanyin safiyar ranar Asabar (12.09.2020) ta sahale musu kan su gudanar da zanga-zangar.

Guda daga cikin wadanda suka hallarci zanga-zangar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewar sun fito don nuna rashin amincewar da matakan da ake dauka kan annobar da ya ce sam babu ita, inda ya ke cewar gwamati na amfani da annobar wajen barnatar da kudaden al'umma da kuma tauye musu hakki.

A share guda kuma, a wani bagaren na birnin na Munich wasu mutane wanda galibinsu matasa ne da kuma 'yan kungiyoyin kwadago sun gudanar da wani gangami na yin Allah wadai da masu adawa da matakan da hukumomi ke dauka na dakile bazuwar cutar ta corona.