1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin abinci na tunkarar duniya saboda Corona

April 1, 2020

Akwai yiwuwar duniya ta fuskanci karancin abinci idan hukumomi suka gaza yin nasara a kan annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aKEp
Afrika Reis
Hoto: picture-alliance/BSIP

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar da ke kula da kasuwanci ta duniya, WTO ne suka sanar da wannan gargadi. Hukumomin sun ce dokar kulle da gwamnatoci a duniya suka sanya tayi mummunar takaita hada-hadar kayan abinci a kasuwannin duniya. 

Kazalika sun ce  a kasashe da dama na duniya jama'a sun yi rige-rigen sayen kayan abinci kafin a sanya musu dokar hana fita saboda annobar Coronavirus, abin da ya kara haifar da karanci da tsadar abinci a wasu wurare. A don haka Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne kasashe su rika barin sukunin yin safarar kayan abinci a kokarinsu na sanya dokar kulle don takaita Coronavirus.