1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

COP26: Shugabanni na ganawa kan dumamar duniya

Mouhamadou Awal Balarabe M. Ahiwa
November 1, 2021

Shugabannin duniya sun fara isowa zauren taron Majalisar Dinkin Duniya mai muhimmanci a kan sauyin yanayi da nufin amincewa da sabbin matakan takaita dumamar yanayi.

https://p.dw.com/p/42QiZ
UN-Klimakonferenz COP26 in Glasgow
Hoto: picture alliance/dpa/AP POOL

Shugabannin kasashe da na gwamnatocin duniya sun yi cikar kwari a birnin Glasgow na Scotland, inda a taron kolin COP26, za a shafe kwanaki 12 ana gudanar da shi. Sa'o'i da dama Fira Minista Birtaniya mai masaukin baki, Boris Johnson da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres suka shafe suna tarbar su cikin raha.

Yawancin shugabannin na duniya sun yi amfani da wannan dama, wajen kare matsayinsu a kan kalubalen sauyin yanayi tare da daukar sabbin alkawuran rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa.

Deutschland RWE Kraftwerk Neurath
Hoto: picture-alliance/dpa/R. Goldmann

Taron na COP26 mai gudana a birnin Glasgow na Scotland, ya fara ne kwana guda bayan da taron kasashen G20 mafiya karfin masana'antu suka gaza cimma matsaya kan burin dakatar da fitar da iska mai gurbata muhalli nan da shekara ta 2050. 

 

Dama dai Boris Johnson na Birtaniya, ya yi gargadi a jajibirin taron dangane da amfani da abin da ya kira dama ta karshe ta iyakance dumamar yanayi zuwa ma’aunin digiri na celcius 1.5, yana mai cewa idan taron Glasgow ya gaza cimma manufa, to za a mai da hannun agogo baya.

Tuni ma 'yar gwagwarmayar yaki da sauyin yanayi 'yar kasar Sweden, Greta Thunberg, ta nemi miliyoyin magoya bayanta da su sanya hannu a kan budaddiyar wasika saboda suna zargin shugabannin da cin amana.

Dama dai masu fafutukar ganin an alkinta yanayi sun gudanar da zanga-zanga a birnin na Glasgow, don nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda shugabannin duniya suka kasa daukar wannan matsala da muhimmanci.

England - Oxfam Protest während COP26
Hoto: Lee Smith/REUTERS

Da dama daga cikin su  sanye da fuskokin mutum-mutumin shugabanni, ciki har da Shugaba Biden na Amirka da Angela Merkel ta Jamus suna ta rera wakoki a lokacin da suke taka sayyada. Masu fafutuka na kungiyar Oxfam na daga cikin wadanda suka nuna fushinsu kan yadda shugabannin ke sako-sako da matsalar dumamar yanayi.