COP23: Shekarar 2017 ta zamo mai zafi
November 13, 2017Talla
Kwararrun sun bayyana haka ne a wajen taron sauyin yanayi na COP23 da ke wakana a nan birnin Bonn.
A cewar Corinne Le Quere, kwararriya kan sauyin yanayi kuma darakta a cibiyar bincike kan sauyin yanayi ta Tyndall a jami'ar East Anglia a Ingila kuma jagorar binciken, abin da suka gano abin takaici ne, kuma mafita ita ce bin sharuda da shawarwari da kwararrun ke bayarwa kan kare muhallin.
A cewar kwararrun muddin ana samun tan biliyan 41 na C02 kamar a wannan shekara ta 2017 zai wahala a rage dimamar duniya da digiri biyu da ake fata.