1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta goyi bayan auren jinsi daya

Ramatu Garba Baba
March 10, 2023

Cocin Katolika a Jamus ya amince ya jagoranci bukukuwa na sanya albarka ga wadanda suka yi auren jinsi guda, daya daga cikin jerin sauye-sauye da darikar ke son aiwatarwa.

https://p.dw.com/p/4OX52
Deutschland Katholische Kirchen segnen gleichgeschlechtliche Paare in einer landesweiten Veranstaltung
Hoto: Andreas Rentz/Getty Images

A hukumance, Cocin Katolika a Jamus ya amince ya jagoranci bukukuwa na sanya albarka ga wadanda suka yi auren jinsi guda. A wannan Juma'ar aka cimma wannan matsayar a kuri'ar da aka kada, inda daga cikin limamai kimanin 202, 176 suka goyi bayan kudurin amma sha hudu suka ki amincewa sai kuma wasu goma sha biyu da suka yi rowar kuri'arsu.

Daga watan Maris na shekarar 2026 za a soma aiki da kudirin a hukumance. An dai jima ana kai ruwa rana kan wannan batun a sakamakon adawa daga masu kin amincewa da aure a tsakanin jinsi guda, wanda wasu manyan kasashen Turai suka amince da shi tun a shekarun baya.