Cinikayyar makamai tsakanin Siriya da Rasha
July 11, 2012Wani jami'in babban hukumar kula da harkokin safarar makamai zuwa ƙetare a ƙasar Rasha ya sanar- a wannan Larabar cewar Rasha ta ƙudiri anniyar miƙawa ƙasar Siriya na'urorin bada kariya ta sararin samaniya , kuma ba ta da wani shirin sanya takunkumin sayan makamai ga ƙasar ta Siriya wadda take da dangantakar ƙut-da-ƙut tun zamanin tarayyar Soviet.
Kanfanonin dillancin labarai sun ruwaito Vyacheslav Dzirkaln, muƙaddashin darektan hukumar kula da harkokin dangantaka ta fuskar soji na ƙasar Rasha yana cewar za su ci gaba da mutunta ƙwangilar da suka sanyawa hannu na baiwa Siriya na'urorin bada kariya ta sararin samaniya, kuma bai ikamata wani ya tuna cewar Rasha za ta katse hulɗar cinikayyar makamai da na fasahar soji da Siriya ba.
Wannan bayanin dai yana zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan da jami'an gwamnatin Rasha suka sanar da cewar ba za su sake ƙulla wata yarjejeniyar cinikayyar makamai tare da ƙasar ta Siriya ba.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu