1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hancin da rashawa a kamfanin man Najeriya

June 27, 2012

Gwamnatin Najeriya ta aiwatar da garambawul a kamfanin kula da albarkatun man ƙasar NNPC a wani mataki na yaƙi da cin hanci.

https://p.dw.com/p/15MwZ
A photograph made available 19 August 2010 shows the Chevron oil facility under contruction in Escravos, 56 miles from Warri in the oil rich Niger delta region of Nigeria 17 August 2010. Nigeria is the fifth largest exporter of oil to the United States and the largest producer of oil in Africa. For decades, thousands of spills across the fragile Niger Delta have hampered the livelihoods of fishermen and farmers, contaminated water sources and polluted the ground and air. Approximately 300 spills are estimated each year. Some are small and some are continuous leaks but compounded they continue to pollute the delta. EPA/GEORGE ESIRI Schlagworte Fabrik, Erdöl, düster, Ufer, Wolken, Schiff, dunkel, Öl, Wirtschaft, Himmel, Schiffe, Natur, Industrie, Verkehr, Unternehmen, Gewässer
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayinda ake jan daga a game da hukunta mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a harkar man fetir din Najeriya, gwamnatin ƙasar ta yi garambawul a kamfanin kula da albarkatun man ƙasar NNPC inda aka kori babban Daraktan kamfanin a abinda  ke nuna daukan sabon salo ga yadda ake gudanar da harkokin kamfanin na NNPC  da ma matsin lamba na hukunta wandan ake zargi da cin hanci a harakar man ƙasar.

Matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na sallamar babban daraktan kamfanin kula da albarakatun man fetir ɗin Najeriya da ma wasu manyan daraktocin kamfanin  tare da naɗa Dr. Andrew Yakubu a matsayin sabon babban daraktan NNPC ɗin bai kasance da bazata ba, sanin irin ja in ja da aka daɗe ana yi a game da yadda shugabanin suke gudanar da harkokin man Najeriyar, da bincike ya nuna sama da faɗi da aka yi a yadda aka gudanar da batun kuɗaɗen tallafin man fetir.

Koda yake shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan ya bayyana wannan mataki da ya ɗauka a matsayin ci gaba da aiwatar da manufofi na ci gaba, to sai dai ga irin kalaman da yayi amfani da su na nuna godiya ga tsoffin shugabanin da ke tsakiyar zargin yin ba dai dai ba a harakar man Najeriyar ya sanya Comrade Abbayo Nuhu Toro na ƙungiyar ƙwadagon Najeriya da suka kasance kan gaba a kan matsawa gwamnati ya bayyana da cewa lamari ne da basu lamunta ba.

**ADVANCE FOR MONDAY, JULY 5** In this June 20, 2010 photo, local residents stand around a broken-down Exxon Mobil oil manifold in Bodo City, in the oil-rich Niger Delta region of Nigeria. As U.S. officials now work to stanch the flow from the Gulf Coast spill, Nigeria remains mired in spills after 50 years of production by foreign firms eager for the country's easily refined fuel. Environmentalists estimate as much as 546 million gallons of oil have spilled into the country's Niger Delta during that time, roughly at a rate comparable to one Exxon Valdez disaster per year. (ddp images/AP Photo/Sunday Alamba).
Hoto: AP

Buƙatar hukunta dukkan masu hannu a baɗakalar

Sanin cewar an gudanar da wannan sauyi ne a dai dai lokacin da gwamnatin ke ci gaba da fuskantar matsatin lamba na lallai sai ta hukunta ɗaukacin mutanen da ake zargi da yin sama da fadi da kudadden tallafin man fetir a ƙasar, duk kuwa da kace nace da lamarin ke haifawar. Irin wannan mataki na sallamar shugabanin da ake zargin suna da hannu dumu dumu a batun cin hanci da rashawa a Najeriya da a mafi yawan lokuta a kan mance da batun ya sanya tambayar shin mecece mafita?  Abinda injiniya Haruna Mohammed ya bayyana da cewa mafita dai guda ce:

A yayin da gwamnatin ke ci gaba da fuskantar matsin lamba a kan wannan harkar, abin jira a gani shine ko gwamnati zata iya hukunta wadanda ake zargi a dai dai lokacin da take ci gaba da gudanar da sauye-sauye a fanin man fetir ɗin ƙasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Mohammad Nasiru Awal