1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Transparency: Cin hanci ya yi kamari a duniya

January 23, 2020

A sabon rahotonta na shekara-shekara da ta bayar, kungiyar Transparency International ta ce kasashe masu arzikin masana'antu ba su samu wani ci-gaba na a zo a gani, a yaki da cin hanci da rashawa ba.

https://p.dw.com/p/3WjW8
Daya daga cikin ofisoshin Transparency International da ke Turai
Daya daga cikin ofisoshin Transparency International da ke TuraiHoto: DW/C.Vieira Teixeira

A bara an fuskanci zanga-zagnar adawa da matsalar cin hanci da rashawa a kasashe irin su Iraki da Chile da Labanon. Sabon rahoton shekara-shekara da kungiyar yaki da cin hanci da rashawa wato Transparency International ta fitar na nuni da cewa mafi akasarin kasashe 180 da ta gudanar da bincike a cikinsu, ba su samu wani ci-gaba a yaki da cin hanci ba, abin da ya sanya shugabar kungiyar, Patricia Moreira nuna takaicinta, tana mai cewa muddin ana son a kawo karshen matsalar ta cin hanci da rashawa a kuma inganta rayuwar jama'a, to dole a yi duba a dangantaka tsakanin 'yan siyasa da hada-hadar kudade masu yawa.

A tsakanin kasashe masu tagomashin tattalin arziki ma a cewar rahoton, ba ga kyautatuwar al'amura ba, inda ma a kasashe hudu daga cikin bakwai na mafiya arzikin masana'antu wato Kanada da Faransa da Birtaniya da kuma Amirka, matsalar karuwa ta yi. Jamus da Japan kuwa matsayinsu bai canja ba, amma Italiya ta samu ci-gaba idan aka kwatanta da shekarar 2018.

Rikici kamar a kasar Somaliya na kawo tsaiko a yaki da cin hanci
Rikici kamar a kasar Somaliya na kawo tsaiko a yaki da cin hanciHoto: picture-alliance/AP/F.A. Warsameh

Kungiyar na ba da maki da 0 inda cin hanci ya yi tsanani, da kuma maki 100 inda babu cin hanci kwata-kwata. A bana kasashen Denmark da New Zealand ne suka zo na daya da maki 87, wato sun fi kowace kasa samun ci-gaba. Jamus ta samu maki 80 dai dai da na shekarar 2018. Ko da yake matsayinta ya daga da maki 2, amma a cewar Transparency wannan ba wani abin a zo a gani ba ne.

Masana na alakanta cin hanci da rashin zaman lafiya, ganin yadda matsalar ta yi kamari a kasashe masu fama da rigingimu, inji Marwa Fatafta da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a kungiyar ta Transparency International.

"Kasashen da ke kasa-kasa a jerin su Siriya da Somaliya da Sudan da kuma Yemen. Abin lura a nan shi ne wadan nan kasashen na fama da rikice-rikice da yake-yake, abin da ke nuni a fili, alaka tsakanin cin hanci da rashin zaman lafiya."

Yadda wasu kasashen ke zanga-zangar nuna adawa ga cin hanci
Yadda wasu kasashen ke zanga-zangar nuna adawa ga cin hanciHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Su ma kasashen Afirka na Kudu da Sahara har yanzu ba su samu wani ci-gaba a yaki da cin hanci ba. Daya daga cikin dalilan shi ne duk da arzikin karkashin kasa, manyan kamfanoni na ketare da ke aiki a yankin, ba sa amfani da ribar da suke samu suna zuba wa a yankin, inji Mokgabo Kupe mai lura da aikin kungiyar a kasashen Afirka na Kudu da Sahara.

"Kasashen Afirka na fama da talauci duk da arzikin ma'adanai. Ko da yake akwai dalilai masu yawa, amma a gani-na babban dalilin shi ne mafi yawan kamfanonin ketare a Afirka ba sa zuba jarin ribar da suke samu a Afirka ba sa kuma shiga cikin aikin raya kasa. Gwamnatoci ba sa ware isassun kudade a fannin kiwon lafiya da na yaki da cin hanci."

Ko da yake ba a ga wani ci-gaba na a zo a gani a duniya baki daya ba, amma jama'a a kasashe da dama na zanga-zangar nuna kyamar cin hanci, abin da a ganin Transparency International zai kai ga samun canji na sahihi nan gaba.