1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya za ta yi bincken harin Al-Shabab

Suleiman Babayo AS
August 22, 2022

Gwamnatin Somaliya ta yi alkawarin rashin rufa-rufa kan bincike hari a otel da tsagerun Al-Shabaab suka kai a Mogadishu babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4FtGN
Somaliya- Jami'an tsaro suna sintiri a birnin Mogadischu bayan hari a otel
Jami'an tsaron SomaliyaHoto: Farah Abdi Warsameh/APdpa

Firaminista Hamza Abdi Barre na kasar Somaliya ya yi alkawarin gwamnati za ta tabbatar da adalci kan binciken harin ta'addaci na kungiyar Al-Shabaab mai ikirarin jihadi ta kai na mamaye wani otel da ke birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar.

Firaminista ya nemi 'yan kasar su hada kan wajen kawar da tsagerun kungiyar ta Al-Shabaab masu dangantaka da Al-Qaeda wadda ta kwashe shekara da shekaru suna tayar da kayar baya. Mutane fiye da 20 suka mutu sakamakon harin wannan wasu fiye da kusan 120 suka jikata, kafin daga bisani 'yan sanda suka kusta wajen kawo karshen mamaya na tsagerun.

Wannan harin ke zama mafi muni da kungiyar ta kai tun lokacin da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somaliya ya dauki madafun iko a watan Mayu.