1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas game da warware rikicin Libiya

Ahmed Salisu
February 24, 2020

'Yan majalisar dokokin na kasar Libiya da suka fito daga yankunan da Janar Khalifa Haftar ke iko da su sun ce ba za su shiga tattaunawar wanzar da zaman lafiya ta kasar ba wadda za a yi da twarorinsu na Tripoli.

https://p.dw.com/p/3YLTu
Libyen Parlament
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Elmhedwi

'Yan majalisar wanda galibinsu suka fito daga gabashin kasar sun ce ba za su shiga wannan tattaunawa ba kasancewar Majalisar Dinkin Duniya ba ta amince da jerin sunayen wakilansu da mika don shiga tattaunawar ba.

A ranar Larabar da ke tafe ce dai aka tsara yin wannan zama sai dai ga alama hakan ba za ta faru ba duba da irin matsayin da 'yan majalisar na bangaren Khalifa Haftar din suka dauka.

Wannan dai ba karamin koma baya bane ga yunkurin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na ganin an kawo karshen tada kayar bayan da Janar Haftar din da dakarunsa ke yi na ganin sun karbe iko da Tripoli babban birnin kasar.