1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wa'adin bukatar yin zabe a Mali

December 24, 2021

A ranar 31 ga watan Disamba ne wa'adin da kungiyar kasashen raya tattalin yammacin Afirka ta ECOWAS a Mali na ta shirya zabuka a kasar a cikin watan Febrairu ke cika.

https://p.dw.com/p/44oBU
Nigeria | ECOWAS Gipfel
Hoto: Präsidentschaft von Niger

Sai dai kuma har yanzu babu alamun gwamnatin rikon kwarya ta sojojin na da niyar yin zabukan.Yayin da ake samun rarabuwar kawunan al'umma a kan batun.

Kungiyar gamayyar tattalin arziki ta kasashen yankin yammacin Afika Ecowas ta ce tana bukatar gwamnatin sojojin Malin da ta bayyana jadawalin zaben, ko kuma ta kakaba mata takunkumi na karya tattalin arziki, bayan takunkumin da aka sakawa wasu jami'an gwamnatin da ke mulki su 149 wadanda aka haramta wa yin balaguro tare da soke kudadensu na ajiya a bankuna.

A ziyara da ya kai a farkon wannan makon a Mali manzon musammun na kungiar ta Ecowas Gooddluck Jonathan tsohon shugaban kasa na Najeriya ya ce bayan tattaunawar da suka yi da jagoran mulkin gwamnatin rikon kwaryar Assimi Goita ya ce ya shaida masa bukatar kungiyar ta ECOWAS.

Putschistenführer Assimi Goita in Mali als Staatschef vereidigt
Jagoran kifar da mulki Assimi Goita Hoto: Habib Kouyate/XinHua/dpa/picture alliance

Gwamnatin ta Mali ta ce sai ta kaddamar  da tattaunawa a tsakanin al'umma kafin shirya zaben amma bin kamar da wuya. Amadou Maiga magatagarda na kwamitin zartaswa na gwamnatin rikon kwaryar na CNT ya ce yanzu ba su da zarafin sauran jam'ar.

"Ya zuwa yanzu muna cikin tattaunawa, sannan doka ba ta ba mu izinin damar sauraron jama'a domin yin nazari a game da batun. Amma ina tsammanin gwamnati na iya kiran taron kwamitin Zartaswa na CNT a zama na musammun, doka ta amince da haka. Da zaran gwamnatin ta kira taron kwamitin da ke kula ba batun zai iya fara sauraran jama'ar ta yadda za a nemi a ji ra'ayin duk  wani mai ruwa da tsaki a cikin lamarin".

Sojojin na Mali wadanda suka yi juyin mulki a cikin kasa da shekaru biyu bayan sauke gwamnatin farar hula ta shugaba Bah N'Daw da firaminitansa Moctar Ouane na da alamun raba gari da kungiyar ta Ecowas a kan wannan batu da suke ganin suna goyon bayan al ummar kasar. Wasu na ganin a ka'idance ba za a ia shirya zaben ba kamar yada Ibrahim Sangho na wata kunguyar da ke da ke lura da  sako ido a kan harkokin zabe ya bayyana.

Mali I Unruhen I Konflikt
Yanayin rashin tsaro na MaliHoto: Michele Cattani/AFP/Getty Images

"A ganinmu, ba mu shirya ba domin zuwa zabe a cikin watan Febrairu na shekara ta 2022 da ke tafe, saboda kafin a je zaben sai an sake dubba rejista masu kada kuria. Za a iya yin aikin sabbinta rejistan a cikin watan Janairu. Watanni biyu bayan haka ana iya yin kiran zaben. Saboda cikin tsarin dokarmu an ce za a iya kiran zabe ne watanni biyu kafin lokacin. A garemu zabe ba zai yiwu ba a watan Febrairu. Amma a cikin watan Maris za a iya yinsa".

Akwai dai sabani tsakanin 'yan kasar ta Mali a kan batun yayin da wasu ke san a tsawaita wa'adin mulkin gwamnatn rikon kwarya, wasu jama'ar na kusa da tsohon shugaban kasar Malin da aka hambarar shekaru biyu da suka wuce kafin juyin mulkin na biyu ke yin gargadi cewar a kiyaye dokar da kudin tsarin mulki kasar ta tanada na watanni 18 na gwamnatin rikon kwarya