Cibiyar Goethe: Bikin cika shekaru 70
An kafa Cibiyar Goethe a ranar tara ga watan Agusta, na 1951. Amma ta habaka cikin hanzari zuwa jakadar Jamus a fannin raya al'adu da harshen Jamusanci.
An kafa ta a birnin Munich
Shekaru shida bayan Yakin Duniya na II, aka kaddamar da Cibiyar Goethe a hukumance, inda ta maye gurbin Deutsche Akademie (DA). A farko, cibiyar ta mai da hankali sosai kan horar da malaman harshen Jamusanci na kasashen waje. A wannan hoton, ana ganin daliban harshen Jamusanci daga Ghana suna yawo tare da iyalan da suka tarbe su Murnau ta jihar Bavaria.
Tallata kyakkyawar dabi'ar Jamus
A shekarun farko, manufar cibiyar ita ce isar da kyakkyawar dabi'a ta Jamus bayan Yakin Duniya na II. A cikin 1952, aka bude cibiyar Goethe ta farko a Athens. Sauran biranen sun biyo baya, ciki har da Mumbai na Indiya (hoto), inda aka sanya wa cibiyar sunan wani masanin Jamus, Max Mueller. A Jamus, an rinka ba da darusa a kayatattun wurare.
Gogen tabon farfaganda da leken asiri
A siyasance, Cibiyar Goethe ta kasance yunkurin Jamus na bude sabon babi, bayan da Deutsche Akademie, da aka kafa a 1925 ya zama cibiyar yada farfaganda ta 'yan Nazi. A shekarar 1945, sojojin mamayar Amirka sun tarwatsa Akademie, saboda suna tunanin cewa "cibiyar farfaganda da leken asiri ne a Turai" ga 'yan Nazi. Wannan hoton yana nuna daliban harshen Jamusanci a Schwäbisch Hall a shekarun 1970.
Jazz da sunan Cibiyar Goethe
A cikin shekarun da suka biyo baya, an ci gaba da bude cibiyoyin Goethe a kasashe dabam -dabam na duniya, misali a Arewacin da Yammacin Afirka, inda, a shekarun 1950 da 1960, sabbin kasashe suka rungumi cibiyar bayan karshen mulkin mallaka. Cibiyar da wakilanta sun shahara a Asiya wajen yada al'adu. Mai busan saxophon na Jamus, Klaus Doldinger (a dama), ya yi kida da mawaka a Pakistan.
Sanya al'adun Jamus a kan taswira
Sauraran sauti ya kasance wani salo nan koyan Jamusanci a shekarun 1980. tun daga lokacin ne cibiyar ta sake sauya dabarunta ta hanyar samar da hanyar sadarwa ta duniya sakamakon hada gwiwa da cibiyoyin al'adun Jamus wadanda ke aiki a kasashen waje. A halin yanzu, cibiyoyi 157 a cikin kasashe 98 suna watsa bayanai kan al'adun Jamus da harshen Jamusanci.
Rufe Goethe don batanci ga Ayatollah
A shekarar 1987, Rudi Carrel, ma'aikacin talabijin daga Netherlands, ya tayar da hankali lokacin da ya gabatar da wasan kwaikwayo wanda ke nuna mutane suna jifar jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Khomeini da rigar mama da dan kamfai. Tehran cikin fushi ta kori jami’an diflomasiyyar Jamus, ta soke tashin jirage zuwa Jamus, sannan ta rufe Cibiyar Goethe da ke kasar Iran.
yaduwa a kasashen Gabas
Bayan faɗuwar katangar karfe, Cibiyar Goethe ta shimfiɗa fikafikanta zuwa gabashin Turai. inda ta kafa cibiyoyi na farko a tsoffin kasashen gurguzu ba tare da kwakkwaran shiri ba. A shekarar 1992, ministan harkokin wajen Jamus, Klaus Kinkel, ya kaddamar da Cibiyar Goethe a Moscow. Amma ba kawai ta girma a wajen Jamus ba, har ma a cikin tsohuwar Jamus ta Gabas.
Karfafa zaman lafiya da fahimtar juna
Hare -haren ta'addanci na ranar 11 ga Satumba 2001 sun ja hankalin Cibiyar Goethe. Daga wannan lokaci, tattaunawa da musayar al'adu suka zama fifiko a gare ta. Yanzu haka cibiyar ta mayar da hankali kan karfafa kungiyoyin farar hula da rigakafin rikici. Wannan hoton yana nuna aikin fasaha da kiɗan "Kunstdisco" a Seoul na Koriya ta Kudu.
Yin rawa tare da mutum-mutumi
A 2016, Cibiyar Goethe ta fara "Kultursymposium Weimar," inda masu tunani daga ko'ina cikin duniya ke tattaunawa kan muhimman kalubale na wannan karni. A 2019, taken bikin ya kasance "Die Route wird neu berechnet" (Ana sake tayar da hanyar), inda mahalarta suka tattauna kan amfanin fasaha a cikin al'umma. A wannan hoton, dan rawa na kasar Taiwan, Huang Yi, yana rawa tare da mutum-mutumi KUKA.
Neman inganta matsayin Jamus
Cibiyar tana shirya "Deutschlandjahre" (shekarun Jamus) tare da ma'aikatar harkokin waje. Burin da aka sa a gaba shi ne ingantawa tare da tallata matsayin Jamus. "Deutschlandjahr" na 2018/19 da ya gudana a Amirka ya samu halartar baki miliyan biyu da suka ziyarci runfuna 2,800. An gudanar da bukukuwan shekarar da ta gabata a Mexico, inda shugabar gwamnati Angela Merkel ta kasance babbar bakuwa.
Bikin shekaru 70 ta yanar gizo
Annobar COVID ta sa cibiyar Goethe rungumar tsarin aiki ta bidiyo ko yanar gizo. Bisa taimakon shugaba Carola Lentz da babban sakatare Johannes Ebert, cibiyar za ta yi bikin cika shekaru 70 da kafuwa a watan Nuwamba na 2021. Za a fitar da littafin Carola Lentz don karrama bikin, kuma wani shafin yanar gizo zai gabatar wa masu karatu da tarihin ban mamaki na cibiyar.