1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban zanga zangar adawa a ƙasar Siriya

July 22, 2011

' Yan adawa na ƙara matsa ƙaimi ga gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad domin yin marabus

https://p.dw.com/p/121oL
Masu zanga zanga a SiriyaHoto: picture alliance / dpa

Masu zanga zangar ƙi jinin gwamnati a ƙasar Siriya sun sake bazuwa akan tituna inda suka gudanar da wani ƙasaitaccen gangami da nufin tilasa wa shugaba Bashar Al- Assad yin marabus.

Sama da mutane dubu ɗari fuɗu ne ƙungiyoyin kare hakin jama'a suka ƙiesta cewa sun halarci gangamin a garuwan daban daban.A garin Homs du da irin matakan tsaron da aka tanada kusan mutane dubu 12 suka amsa kiran yayin da a biranen Dera'a da Damaskas da Jable yanki da ke bakin taku jama'a suka yi cikkar ƙwari akan titunan.jama'ar waɗanda suke cikin ɓacin rai dangane da kisa mafi muni da sojojin suka aikata a ƙwannan nan a garin Homs sun riƙa raira kallamun yin suka ga gwamnatin Bachar- Al -Assad wacce suke neman ganin ta faɗi.

Kuma zanga zangar sun yi mata laƙabi ta nuna alhini ga al'ummar garin Homs.An dai kara kuma aka sha artabuwa kamar yadda aka saba yi a kowa ne makon inda a yankin arewa maso gabacin ƙasar a garin Hassake na yan ƙabilar ƙurdawa sojojin suka yi amfani da hayaƙi mai sa ƙwalla da kuma kulake wajan tarwatsa jama'ar.

Syrien Demonstration gegen Präsident Bashar Assad in Damaskus Vorort
Hoto: dapd

Alex Frank wani jam'in agaji ne ƙasar Faransa dake a birnin Damaskas '' Ya ce yanzu ina tsamanin cewar za ta kasance wa ya fi ƙarfin tsakanin masu zanga zangar da gwamnatin wacce ke amfani da makamai wajan murƙushe boren.''

Sannan kuma wasu rahotannin na cewa sojojin sun kashe mutane 11 a garin Homs da Alep inda wani mai goyon bayan shugaba Assad ya daɓa ma wani mutumin wuƙa a gaban masallaci yayi da ɗaya sojoji ne suka harbeshi har lahira.

Kawo yanzu dai alƙaluman ƙididiga na nuna cewa an kashe mutane kusan guda dubu ɗaya a zanga zangar da yan adawar suka soma tun a tsakiyar watan Maris da ya gabata.

Syrien Demonstration gegen Präsident Bashar Assad in Damaskus Vorort
Hoto: dapd

Alex ya ci-gaba da cewa'' mun gani cewa bayan mutuwar mutane da dama a cikin garuruwa abin sai ci-gaba ya ke yi inda ake samun ƙarin sabbin zanga zangar a wasu garuruwan tare da jama'a masu yawan gaske da ke fitowa

Ƙasar Faransa wacce ta sake yin Allah wadai da kashe kashen jama'a ta hanyar kakakin ministan harkokin wajen ƙasar Bernard Valero ya shaida cewa sojoji da sauran jam'ian tsaron da ke aikata kisa akan fararan fula su san cewa ko ba juma ko ba daɗe zasu fuskanci hukumci.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar