1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban zanga-zanga a Masar

January 26, 2011

A ƙasar Masar an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shugaba Hosni Mubarak da suka kira ɗan kama karya.

https://p.dw.com/p/105d6
Taho mu gama tsakanin 'yan sandan kwantar da tarzona da masu zanga-zangaHoto: AP

A ƙasar Masar an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga a tsakiyar Alƙahira babban birnin ƙasar da kuma birnin Suez da ke gabar tekun kasar. An shiga zanga-zangar ne a rana ta biyu duk da kuwa kamen kamen da dakarun tsaro ke yi. 'Yan sanda sama da dubu 20 ne aka tura zuwa birnin na AlƘahira . An dai haramta gudanar da duk wata zanga-zanga, kuma ƙungiyoyin adawa sun ce an toshe shafukan yanar gizo na Twitter da facebook. Jami'an tsaron ƙasar ta Masar sun ce ana tsare da 'yan zanga-zanga 500. Dubun dubatan jama'a ne dai suka shiga zanga-zangar domin yin kira ga ɗan kama karya Shugaba Hosni Mubarak da ya sauka daga karagar mulki.

Ägypten Protest Januar 2011
'Yan zanga-zanga da suka toshe hanya a birnin AlkahiraHoto: AP

Shafukan yanar gizo na ƙasar ta Masar da na sauran ƙasashen Larabawa na ba da rahotannin da ke nuni da arcewar ɗan shugaba Mubarak Gamal da iyalinsa zuwa ƙasar Birtaniya a asirce. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce gwamnatin Jamus na nuna matuƙar damuwa da rikicin da ake yi a kasar ta Masar tare da yin kira ga dukkan bangarori da su kauce wa tsunduma kasar a cikin tashin hankali.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal