1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban zang- zanga a Siriya

April 29, 2011

Dakarun tsaro a Siriya sun kashe 'yan zanga-zanga guda 15 a garin Daraa da ke kudancin kasar da ak fara nuna adawa da gwamnati a cikinsa

https://p.dw.com/p/116cw
Tankar dakarun tsaro a birnin Dara'aHoto: picture alliance / dpa

Likitocin da 'yan fafutukar kare haƙkin bil Adama sun ce dakarun ƙasar Siriya sun kashe aƙalla mutane 15 a garin Daara da e kudancin ƙasar. Dakarun sun harbe mutanen ne a lokacin da 'yan zanga-zangar suka yi yunƙurin shiga tsakiyar birnin da a cikinsa ne aka fara gudanar da boren nuna adawa da gwamnati. To amma a faɗin ƙasar ta sSya dubban mutane sun take haramcin gudanar da zanga-zanga da aka ayyanar suka bi titunan birane hada da na Damascus . Kungiyoyin kare haƙkin bil Adama sun ce 'yan zanga zanga sama da 500 ne suka rasa rayukansu tun bayan da aka ƙadaddamar da boren nuna adawa da gwamntin Shugaba Assad makonni shida da suka gabata. A dai halin da ake ciki yanzu jami'an ƙungiyar Tarayyar Turai na tattauna yiwuwar aza wa Siriya takunkumin da zai hada da haramcin tafiya da kuma ƙwace kuɗaden ƙasar da ke a bankunan ketare.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman