1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban yaƙi a ƙasar Libiya

May 20, 2011

Jiragen ƙungiyar tsaro ta NATO sun kai hari kan Jiragen ruwa na yaƙin gwamnatin Libiya guda takwas

https://p.dw.com/p/11K9H
Hayaƙi a Jirgin ruwa bayan hariHoto: AP

Gamayyar ƙasashen yammaci na NATO, sun shaidar da cewar Jiragen yaƙin ƙungiyar sun nutsar da Jiragen sojin ruwa guda 8 na shugaban Libiya Muammer Gaddafi. An kai hare-haren haɗin gwiwa akan tashoshin Jiragen ruwan da ke Tripoli, Sirte da Al Khums. A cewar NATOn dai Jiragen na Gaddafi na da alhakin binne Nakiyoyi, waɗanda ke haifar da barazana ga kai agajin gaggawa wa fararen hula. Waɗanda suka gane wa Idanunsu dai, sun shaidarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP tarwatsewar tashar jiragen ruwa da ke birnin Tripoli. Tun a watan Maris ne dai ƙungiyar kawancen tsaro ta NATO, ta karɓi akalar jagorancin aiwatar da kudurin Majalisar Ɗinkin Duniya a Libiya. 

A halin da ake ciki yanzu haka dai, kakakin gwamnatin Libiya ya ƙaryata rahotannin da ke nuni da cewar Uwargidan Gaddafi da 'Yar sa sun tsere zuwa tsibirin Djerba dake ƙasar Tunisia. Kazalika majiyar gwamnatin Tunisiya ta karyata wannan rahoto.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita          : Shehu Usman Shehu