1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban shari'ar Husni Mubarak

June 10, 2013

A cikin tsauraran matakai na tsaro ne dai a wannan Litinin a Masar aka ci gaba da sauraron shari'ar da ake wa tsohon shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/18nGf
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani da ya halarci zaman kotun ya ce a cikin keji ne aka kawo tsohon shugaban Husni Mubarak a dakin kotun da ke cikin ginin makarantar horar da 'yan sanda a birnin Alkahira. Tsohon shugaban da 'ya'yansa biyu wato Alaa da Gamal da kuma tsohon ministan cikin gidan kasar, Habbib al-Adi ana tuhumarsu ne da laifin kashe sama da mutane 800 yayin zanga-zangogin da suka gudana a watannin Janairu da Fabarairun shekarar 2011. Hukuncin daurin rai da rai ne dai aka yanke wa tsohon shugaban tun da farko. An kuma dage zaman yanke wa shugaban hukunci zuwa wani lokaci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal