1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban rikici a Siriya

September 2, 2011

Masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin sun lashi takobin ci gaba da gudanar da zanga-zanga ko ana ha mata ha maza.

https://p.dw.com/p/12RqG
Yan zanga zangar Siriyaasu neman taimakon kasa da kasaHoto: dapd

Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnatin Bashar al-Assad a ƙasar Siriya na shirin gudanar da wani gangami a yau 02.09.2011 bayan sallah juma'a wanda aka yi wa lakabi da sunan "gara a mutu da ganin walaƙanci".

Wannan bore da za a yi ya biyo bayan ƙarin kisan wasu mutane guda bakwai da jami'an tsaro suka aikata a jiya 01.09.2011 a birnin Damaskas da kuma garin HomsKasashen Ingila da Amirka sun ce lokaci ya yi da ƙasashen duniya za su ƙara matsa ƙaimi ga shugaba Bashar al-Assad domin ya yi marabus kamar yadda sakatariyar harkokin wajen Amirka Hilary Clinton ta bayyana:

"Yau dai aka shirya Kungiyar Tarrayar Turai za ta saka takunkumi ga cinikin man fetur din da take yi da Siriyar:"

Kungiyar Tarayyar Turai ita ce ke sayen kusan kashi 95 cikin ɗari na man fetur ɗin da ƙasar ta kan sayar wa kasashen waje.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane
Edita: Halima Balaraba Abbas