1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban hare-haren NATO kan dakarun Libiya

August 5, 2011

Kakakin 'yan tawayen Libiya ya sanar da mutuwar mutane 32 a cikin hare-haren da ƙungiyar NATO ta kai kan dakarun gwamnati

https://p.dw.com/p/12BxK
Wani gini da harin NATO ya lalataHoto: dapd

Wani mai magana da yawon 'yan tawayen Libiya ya ce an samu mutuwar mutane 32 cikinsu har da ɗan shugaba Gaddafi, mai suna Khamis bayan da ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO ta yi luguden wuta. Khamis ya yi aiki ne a matsayin ɗaya daga cikin kwamandodin sojojin Libiya. Kakakin ya ce luguden wutar ya faru ne a wani wuri da ke da tazarar kilomita 60 daga birnin Tripoli. Wani jami'in NATO da ke birnin Naples na ƙasar Italy ya ce yana da wannan labari ko da yake bai ba tabbacin aukuwar hakan ba. A cikin martanin da ta mayar gwamnatin Libiya ta ce musunta mutuwar ɗan Gaddafi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman