1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu goyon bayan sojojin Sudan na zanga-zanga

Suleiman Babayo ATB
October 18, 2021

Ana ci gaba da zanga-zanga kan neman firaministan Sudan ya ajiye aiki yayin da gwamnatin wucin gadin kasar take tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/41p6Q
Sudan I Protest in Khartoum
Hoto: Marwan Ali/AP/picture alliance

An sake samun mutane da dama da ke goyon bayan sojojin Sudan da suka yi zanga-zanga a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar inda suke neman ganin Firaminista  Abdalla Hamdok ya ajiye aiki.

Shi dai Firaminista Hamdok ya shaida wa majalisar zartaswar kasar cewa gwamnatin wucin gadin tana fuskantar rikici mafi hadari tun bayan da masu zanga-zanga suka kawo karshen gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir.

Ita dai gwamnatin wucin gadi ta Sudan tana kunshe da sojoji da fararen hula inda aka tsara za ta gudanar da zabuka zuwa shekara ta 2023.