1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zaɓen raba gardama a kudancin Sudan

January 14, 2011

Ko da yake ana sa ran cewar zaen raba gardama a kudancin Sudan zai ba da goyan bayan allewar yankin ne, amma fa lamarin na tattare da ayoyin tambaya.

https://p.dw.com/p/zxb9
Masu kaɗa ƙuri'ar raba gardama dangane da kudancin SudanHoto: DW/Shinger

A wannan makon dai ƙuri'ar raba gardama a game da makomar kudancin Sudan ita ce ta fi ɗaukar hankalin jaridun na Jamus. A cikin nata rahoton dai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

Satellitenbilder Südsudan Clooney
Akwai matsalar hanyoyin sadarwa a kudancin SudanHoto: picture-alliance/dpa

"Duk da ɗoki da murnar da ake yi game da yiwuwar samun ikon cin gashin kan kudancin Sudan, amma fa abin lura shi ne kasancewar yankin mai mazauna kimanin miliyan takwas da dubu ɗari biyar, ka iya zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da matsalar talauci a duniya. Yankin mai faɗin murabba'in kilomita dubu ɗari shida dake kuma da ɗimbim arziƙin mai ba ya da hanyoyin sadarwa ko ƙwararrun ma'aikata. Bugu da ƙari kuma yanki ne dake ƙunshe da ƙabilu daban-daban da ba su ga maciji da juna, inda a cikin shekaru goman da suka wuce yawan mutane da suka yi asarar rayukansu sakamakon rikice-rikice na ƙabilanci ya ninka yawan waɗanda suka mutu sakamakon yaƙi tsakanin arewaci da kudancin Sudan."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"A daidai lokacin da aka gabatar da ƙuri'ar raba gardama a game da ikon cin gashin kan kudancin Sudan faɗa ya ɓarke tsakanin mayaƙan Misseriya dake samun goyan baya daga arewaci da dakarun ƙabilar Dinka a kudancin Sudan da kuma sojojin haɗa-ka na arewaci da kudancin Sudan a yankin Abyei mai arziƙin man fetur. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, saboda tun a zamanin baya ɗora hannu akan rijiyoyin mai dake yankin ke da muhimmanci ga sassan biyu da ba su ga maciji da juna."

Niger Entführung
A makon jiya aka sace tare da kisan wasu matasa 'yan ƙasar Faransa su biyu a YamaiHoto: AP

A wani mataki na ta'asa da rashin imani a ƙarshen makon da ya gabata an yi garkuwa da wasu matasa 'yan ƙasar Faransa su biyu, waɗanda kuma aka yi wa kisan ba-gaira daga bisani a janhuriyar Nijar, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

"A sakamakon wannan ɗanyyen aiki, a yanzun Faransa ta lashi takobin saka ƙafar wando ɗaya da 'yan ta'adda dake ta da zaune tsaye a yankin Sahel. Waɗannan matasa dake da shekaru 25 na haifuwa ƙungiyar dake kiran kanta wai ƙungiyar alqa'da ta yankin Maghreb, ita ce ke da alhakin sace su da kisansu. A kuma halin da ake ciki yanzu haka ƙungiyar mai taken Aqmi a taƙaice na ci gaba da garkuwa da wasu Faransawa biyar, waɗanda ƙungiyar ta kame su tun a cikin watan satumban da ya wuce. Kazalika a watan yulin da ya gabata sai da ƙungiyar ta kashe wani Bafaranshe mai shekaru 78 da haifuwa saboda Faransar ba ta biya musu buƙatunsu ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Usman Shehu Usman