Ci gaba da shari'ar tsohon shugaban Masar
August 15, 2011Kotun dake sauraren shari'ar tsohon shugaban ƙasar Masar Hosni Mubarak ta ɗage ci gaba da shari'ar har ya zuwa ranar biyar ga watan Satumba. Tsohon shugaban, mai shekaru 83 a duniya, ya yi bayyanar sa ta biyu a cikin kotu kwance akan gadon asibiti.
Alƙalin da ke sauraren shari'ar, wadda ta haɗa da 'ya'yan tsohon shugaban su biyu, ya faɗaɗa tuhumar ta ƙunshi tsohon ministan kula da harkokin cikin gidan ƙasar ta Masar Habib el-Adly. Hakanan kuma alƙalin ya ce daga yanzu ba za'a ci gaba da nuna shari'ar - kai tsaye ta na'urorin telebijin ba.
Ana dai tuhumar tsohon shugaban na Masar ne da hannu wajen kissar masu boren adawa da gwamnati yayin zanga-zangar adawar da ta kifar da gwamnatin nasa a tsakanin watan Janairu da kuma Fabrairun bana. Tuni dama tsohon shugaban ya yi watsi da zarge-zargen.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdullahi Tanko Bala